Watsi Da Tashoshin Arewa: Kungiyoyin Arewa Sun Yi Kiran Kauracewa DSTV

Gamayyar kungiyoyin Arewa 19 sun yi kira da babbar murya ga Jihohin Arewacin Najeriya da su dauki matakin kauracewa kallon DSTV, sakamakon kememe da kamfanin ya yi na sanya tashoshin Talabijin na Arewa a cikin manhajar shi.

Bayan da gamayyar kungiyoyin Arewa ta rubuta takardar koke akan watsi da tashoshin Talabijin na Arewa da DSTV ke yi a jadawalin ta a ranar 10 ga Watan Janairun shekarar 2021, Hukumar dake kula da kafofin yada labarai ta kasa NBC ta shirya wani zama da kamfanin na DSTV a ranar 18 ga watan Maris, inda aka daddale cewar kamfanin zai sanya wasu tashoshin Arewa a jadawalin shi.

Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun Kungiyoyin Arewan Abdul-Azeez Suleman ya fitar a Abuja, ya bayyana takaicin shi da cewar har ya zuwa wannan lokaci DSTV ya gaza cika alkawarin da ya yi na sanya tashoshin Talabijin na Arewa a jadawalin shi.

Gamayyar kungiyoyin Arewan sun bukaci hukumar NBC ta tabbatar DSTV ta mutunta wannan yarjejeniya da aka yi kafin su ?auki mataki wanda ba zai yi kyau ba.

Related posts

Leave a Comment