Ketare: Kotu Ta Bada Umarnin Tono Gawar Mugabe

Wata kotun majistiret a Zimbabwe ta ce za a iya tono gawar tsohon shugaban kasar marigayi Robert Mugabe bayan wani basaraken gargajiya ya ce binnewar da aka yi masa ta keta dokokin al’adun gargajiyarsu.

An binne Mugabe, wanda ya mutu a shekarar 2019 yana da shekara 95 a makabartar iyalinsa. Sai dai a watan Mayu wata ta saurari karar wani basarake da ya ce binnewar da aka yi masa ta karya dokokin al’adunsu, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters a wancan lokacin.

“Na bayar da umarni ga wadanda doka ta bai wa ikon tono gawar marigayi Robert Mugabe daga makabartar Kutama sannan a sake binne ta a Makabartar Gwaaraza da ke Harare,” a cewar kwafin hukuncin kotun da aka bayar da harshen Shona kamar yadda Reuters ya rawaito.

Iyalan Mugabe sub kalubalanci hukuncin, sai dai kotun ta majistiret ta yi watsi da maganarsu.

Mai yiwuwa iyalan sun daukaka kara zuwa Babbar Kotu, a cewar wakiliyar BBC Shingai Nyoka.

Mugabe ya jagoranci Zimbabwe daga lokacin da ta samu ‘yancin kai a 1980 zuwa 2017, lokacin da aka hambare shi daga mulki.

Related posts

Leave a Comment