Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta kammala dukkanin shirye shiryen ta na sayen wani yaro mai shekaru 4 mai suna Zayn Ali Salman a matsayin ?an wasan kungiyar.
Hankalin shugabannin kungiyar ta Arsenal ya kai ga yaron ne a wani wasan ?wallon ?afa da yayi, inda suka nemi wakilan da su amince yaron ya ziyarci birnin London.
A tarihin Shahararriyar ?ungiyar kwallon kafan Zayn Ali Salman ya kasance ?an wasa mai ?ananan shekaru da ta ta?a saye, kuma sayen nashi ya ?auki hankalin duniya.
Kocin Kungiyar ta Arsenal Mikel Arteta ya bayyana yaron a matsayin wata ajiyar Allah ta fuskar wasanni wanda zai kafa tarihi a duniyar kwallon kafa.
