Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya ta fada wa Rasha cewa za ta buga wasannin share fagen zuwa gasar cin kofin duniya ne da sunan ‘Football Union of Russia’, saboda kutsawa Ukraine da ta yi.
Hakama FIFA ta ce ba za ta yi amfani da tutar Rasha ba, kuma zata buga wasannin ne a wata kasa daban.
To amma tuni kasashe da dama sun bayyana cewa ba za su buga wasa da Rasha ba.
Dama Rasha na da wasan share fagen zuwa Qatar 2022 da Poland, kafin ta buga da Chek Refoblik ko Sweden a watan Maris.
A ranar Alhamis ne Shugaba Vladimir Putin ya kutsa da sojojinsa Ukraine mai makwabtaka kuma tun a lokacin ake gwabza yaki.
