Labarin dake shigo mana daga Hedikwatar tsaron ?asa DHQ ta bayyana cewa rundunar ‘Operation Hadin Kai’ ta ci gaba da samun nasarori a yaki da Boko Haram da ‘yan bindiga inda a cikin makonni biyu da suka wuce ‘yan ta’adda 466 sun mika wuya.
Darektan yada labarai na hukumar manjo-janar Bernard Onyeuko ya sanar da haka da yake bayanin aiyukkan da dakarun suka yi daga ranar 10 zuwa 24 ga Fabrairu ranar a Abuja.
Onyeuko ya ce ruwan bamabaman da sojin sama da na ?asa suka yi ya taimaka wajen sadaukar da kai da ‘yan ta’adda 466 suka yi suka mika wuya. Cikin su akwai maza 120, mata 137 da yara 209.
Bayan haka Onyeuko ya ce ruwan bama-baman da rundunar sojin sama ta yi ranar 11 ga Fabrairu a Marte jihar Borno ya kashe wani shahararren dan bindiga Muhammed Yusuf da wasu yaran sa.
“Dakarun sun kashe ‘yan bindiga 10, sun kama 26 sannan sun kwato makamai da motocin bindiga guda hudu.
Daga nan rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ sun kashe wani shahararren dan bindiga Dogo Umaru a dajin yankin jihar Zamfara.
