Wadata Sojoji Da Makamai Ne Zai Magance Matsalar Tsaro – Babangida

Tsohon shugaban ?asa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, yayi kira ga gwamnatin yarayya ta horas da jami’an soji tare da wadata su da makamai na zamani domin magance matsalar tsaro dake addabar kasar nan.

Babangida wanda ya nuna matu?ar damuwarsa kan halin da ake ciki na rashin tsaro yace ya kasance yana taimakawa da bayar da shawarwari ga gwamnati ba tare da kowa ya sani ba, domin a gudu tare a kuma tsira tare.

Tsohon Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a gidanshi dake Mina babban birnin Jihar Neja ranar Sallah, Yace ya zama wajibi ga kowane ?an ?asa ya nuna goyon bayansa ga gwamnati da jami’an tsaro domin su kawo ?arshen matsalar tsaron da ake fama da shi a wannan ?asa tamu Najeriya.

Yayin da aka tambayesa ko yana ganin wa?anda ke kan madafun iko suna wasa da lamarin kawo ?arshen matsalar tsaro, Babangida yace: “Akwai abubuwa da yawa da ya kamata su gyara, idan suka amince suka sake zama da tunani akan lamarin, ina da ya?inin zasu samu nasara cikin sauki.”

Yayin da yake jawabi akan abinda ya kamata masu mulkin ?asar nan a yanzun suyi, yace: “Ku samar wa soji duk abinda suke bu?ata, sannan ku tunasar dasu cewa wannan ?asar su ce, kuma basu da wata ?asa data fi ta.”

“Sojin Najeriya na bu?atar makamai irin na zamani kuma suna bu?atar a horas da su. Ba wai kawai a siyo makamai a mi?a musu ba, ya zama wajibi a horas dasu yadda zasu yi amfani da makaman.”

A ?o?arin da yake na taimakawa da shawarwari ga gwamnati domin ganin an kawo ?arshen wannan matsala, wadda a yanzun take nema ta mamaye mahaifarsa, jihar Niger, Babangida ya cigaba da cewa: “Muna bada shawara dai-dai gwargwado, bamu yayata duk abinda muka fa?awa gwamnati.

Ya zama wajibi mu ha?a kan mu, mu taimakawa wa?anda ke kan madafun iko, dukkan mu muna aiki ne don cimma kudiri ?aya.” “Matsalar tsaro da rashin zaman lafiya, kowace gwamnati tana da nata ?alubalen, ina tuna yadda muka yi ya?i na tsawon shekara uku, a lokacin mutane sun taimaka wa gwamnati, gwamnati ta yi iya bakin ?o?arinta.”

“Ba wai a Najeriya ne ka?ai ake samun irin wannan matsalar ba, kasashe da yawa sun shiga irin wannan, wasu saida suka ?auki shekara 10 kafin su samu nasarar magance komai, ina da ya?inin cewa watarana Najeriya zata fita daga cikin wannan ?angin.”

Related posts

Leave a Comment