Tura Ta Kai Bango: Gwamnati Za Ta Fara Amfani Da Mutum-Mutumi A Yakar Ta’addanci

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar Dattawa ta ce Ma’aikatar Sadarwa ta kafa wata cibiya da za ta rika aiki da Mutum-Mutumi da basirar na’ura don yaki da matsalolin tsaro a kasar.

Najeriya dai na ci gaba da fama da matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane don kudin fansa da hare-haren ‘yan bindiga musamman a arewacin kasar da ma ayyukan masu ikirarin jihadi a arewa maso gabashin kasar.

Kawo yanzu, sama da dalibai 1,000 ne aka sace daga makarantu a arewacin Najeriya tun daga watan Disamban 2020.

A shekarun baya matsalar tsaron ta fi ?amari ne a yankin Arewa maso gabashin kasar inda fitinar Boko Haram ke ta’azzara, amma a ‘yan shekarun nan abubuwa sun sauya inda sashin Arewa maso yammacin kasar ya shiga tasku dalilin bala’in ‘yan Bindiga.

Related posts

Leave a Comment