Jagoran jam’iyyar APC na kasa Alhaji Bola Ahmad Tinubu, ya yi gyaran fuska akan kalamin da yayi na a ?auki sojoji matasa Miliyan 50 aiki, inda ya ce ba yana nufin gwamnatin tarayya ta ?auki matasa 50 miliyan aikin soja ba, 50,000 yaso fa?a bakinsa ya ku?uce.
Bola Tinubu yayi gyara kalamansa ne a ranar Talata inda yace su?utar baki ne yasa ya fa?i haka amma shi mutum 50,000 ya so cewa, a domin haka ya bukaci jama’a suyi mishi uzuri.
An ga Tinubu na fa?a a wani bidiyo da ya mamaye kafafen sada zumunta cewa, gwamnatin tarayya ta ?auki matasa 50 miliyan aikin soja don ta ?arfafa ya?in da take da ta’addanci wanda ya dabai-bayeta.
Jagoran jami’iyya mai mulki ya fa?i haka ne a wajen taron bikin cikarsa shekaru 69 a duniya ranar Litinin, 29 ga watan Maris. “Ku ?au matasa miliyan 50 aikin soja” Tinubu ya fa?a a wajen taron yana mai ?arawa da cewa duk abinda zasu ci muna da su a ?asar nan.
Mai taimaka wa Tinubu ta fannin ya?a labarai, Tunde Rahman, ya shaida cewa, yana nufin gwamnati ta ?auki matasa 50,000 ne ba miliyan 50 ba kamar yadda ya fa?a a baya.
Sai-dai tun daga lokacin da ya yi wancan magana, ta jawo hankulan mutane da yawa a kafafen sada zumunta musamman tuwita.
