“Tun bayan da na musulunta nake fuskantar manyan matsaloli a rayuwata, tuni Iyaye na suka sallama ni, Musulmi da nake cikin su kuma ba su nuna mini soyayyar da ta kamata ba, masu ku?i sun mayar da ni wata hanya ta kashe ?walama kawai”.
Kalaman Muneerat Abdulsalam kenan a wani faifan bidiyo da ta fitar tana hawaye, inda take bayyana irin halin ?uncin da ta shiga, dalilin da ya sanya har ta yi kato?arar da tayi na i?irarin ficewa daga addinin Musulunci.
“Wasu ne suka fusata ni, suna yi min gorin Musulunta, suna kira na Yare, shi ya sa na ce na bar Musulunci! Amma har yanzu ni Musulma ce, kuma ina fatan mutuwa a cikin addinin Musulunci”.
Muneerat Abdulsalam ta kara da cewa “saboda soyayyata da Musulunci na yi hannun riga da mahaifina domin shi ba musulmi bane, na guji ‘yan uwana na jini na dawo cikin Hausawa.
Sannan kuma tunda na musulunta babu wanda ya ja ni a jiki, sai kyama ta da gori da ake yi min, kuma duk manyan da suke bibiyata babu wanda yake nema na da aure saidai su nemi na zo su yi zina da ni su biya ni”.
