Kaduna: Sarki Bamalli Ya Karbi Sandar Sarauta

A ranar Litinin 09/11/2020 ya zo daidai da ranar da ake baiwa Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli sanda na tabbatar masa da Sarki mai cikakken iko a Masarautar Zazzau.

Taron ya wakana ne a filin sukuwan dawaki da ke Sabon Gari cikin garin Zaria, inda Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya ba shi sandar.

Taron ya samu halartar manyan baki da suka hada da Sarkin musulmi Mai Alfarma Sa’ad Abubakar da manyan baki da dama.

Muna addu’a Allah ya sa a tashi lafiya, ya baiwa Sarki ikon yin adalci ga al’ummar masarautar Zazzau da jihar Kaduna da Nijeriya baki daya. Allah ya bashi ikon hada kan gidajen Sarautar Zazzau kamar yadda Marigayi Alhaji Dr Shehu Idris ya yi a lokacin rayuwarsa. Amin.

Related posts

Leave a Comment