CORONA: Najeriya Ta Karbi Rigakafi Daga ?asar Rasha

Gwamnatin Tarayyar Najeriya a ranar Juma’a ta karbi samfurin rigakafin cutar korona na ?asar Rasha. Jakadan Rasha a Najeriya, Alexey Shebarshin ne ya mika wa ministan lafiyar Najeriya, Osagie Ehanire rigakafin yayin ziyarar da ya kai ma’aikatar lafiyar a babban birnin tarayya Abuja.

Wannan na ?unshe ne cikin wata sanarwa mai ?auke da sa hannun mai magana da yawun ma’aikatar, Olujimi Oyetomi.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce ?asar sa ta amince da wani rigakafi da ke bayar da kariya daga coronavirus wanda hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, daga baya ta ce za ta yi nazarin ingancin rigakafin.

Ehanire ya ce ” ba tare da ?ata lokaci ba za a mika rigakafin ga Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna, NAFDAC, da Cibiyar Binciken Magunguna ta Najeriya da wasu hukumomin don tabbatar da ingancinsa kafin a duba yiwuwar amfani da shi.
A cewar al?allumar da hukumar da?ile cututtuka masu ?aduwa ta Najeriya, NCDC ta fitar a daren Alhamis, fiye da mutum 50,000 ne suka kamu da coronavirus. Al?alluman sun kuma nuna kimanin mutum 1,000 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon kamuwa da cutar ta korona.

Related posts

Leave a Comment