Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnan Jihar Nasir El-Rufai ya nemi gafara al’umma bisa hare-haren da ‘yan bindiga ke ci gaba da salwantar da rayukan a yankunan Jihar Kaduna, musamman harin da aka kai wa jirgin kasa a ranar Alhamis.
Gwamnan, wanda cikin yanayi mai cike da damuwa ya ce ha?i?anin gaskiya yana cikin matu?ar bakin ciki saboda rabonsa da ya yi bacci tun ranar Alhamis, kuma ba ya iya bacci ko da ya sha maganin bacci saboda tsananin tashin hankali.
El-Rufa’i ya yi wa?annan kalamai ne lokacin da ya je karamar hukumar Giwa domin bai wa al’umma hakuri da ta’azziya da jaje bisa abubuwan da ke faruwa.
Ya kai ziyarar ne ranar Alhamis ?ar?ashin rakiyar mataimakiyarsa Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe da kuma wasu mukara?an gwamnatinsa.
A wani sa?on murya da masu taimaka wa gwamnan kan ya?a labarai suka fitar, sun ce gwamnan ya ce hakkin shugabanci abu ne da wata rana zai tashi ya tsaya gaban Ubangiji domin ya yi bayyani kan abubuwan da ke faruwa da abubuwan da ya aiwatar.
“Hakkin shugabanci kamar yadda malaman addinin suka fada, abu ne wanda wata rana zan tsaya gaban Allah SWT in yi bayanin me na yi don tabbatar wa?annan abubuwa ba su faru ba.
“Ina tsoron wannan rana da zan tsaya a gaban Allah na fadi me na yi, me zan iya cewa mun yi? Saboda haka dole mu ro?i gafararku da afuwarku domin a gwamnatance mu muka kasa.
