Rahotanni daga Sokoto birnin Shehu na bayyana cewar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar wanda shi ne shugaban majalisar koli kan harkokin addinin Musulunci ya bu?aci al’ummah Musulmi su soma duba sabon watan Azumin Ramadana a yau Juma’a.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da fadar Sarkin Musulmin ta fitar dauke da sa hannun babban jami’i a majalisar, Arc. Zubairu Haruna Usman-Ugwu.
Sanawar ta umarci al’umma su soma duba sabon watan daga yammacin Juma’a 1 ga watan Afrilun, 2022, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Sha’aban shekara ta 1443 bayan hijira.
Idan aka yi nasarar ganin watan a yau Juma’a to za a tashi da Azumi ranar Asabar a matsayin 1 ga watan Ramadana kenan. Idan kuma ba a ga wata ba to 1 ga watan Ramadan zai kasance Lahadi 3 ga watan Afrilu, a cewar sanarwar.
