Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan harkokin soji, Sanata Ali Ndume, ya soki lamirin shugaban kasa Muhammadu Buhari da hafsoshin tsaron kasar kan tabarbarewar tsaro a kasar.
Ndume Sanata mai waklitar Borno ta Kudu a majalisa Dattawa kuma jigo a jam’iyyar APC ya yi sukar ne dangane da mummunan harin da aka kai gidan yarin Kuje a ranar Talata, lamarin da ya yi sanadiyar tserewar ‘yan ta’adda da dama, ya ce shugabancin kasar ya gaza a babban kudirin sa ga ‘yan kasa.
A wata hira da yayi a gidan talabijin na Channels, ya ce da harin ba zai yiwa yan ta’addan sauki ba inda gidan yarin ya kasance da isassun makamai da isassun ma’aikata. “Na tabbata da jam’ian tsaro sun gaggauta kai dauki da an samu nasarar dakile harin amma sun dauki tsawon sa’o’i hudu a gidan yarin babu taimako daga koina,” in ji Sanatan.
Sanata Ndume ya koka da yadda gwamnati mai ci a yanzu ke sanya mutanen da ba su iya aiki ba shugabanci a wurare masu muhimanci.
