2023: Musulmi Tinubu Zai Dauka Mataimaki – Ganduje

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamanna jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya amince zai dauki Musulmi a matsayin mataimakinsa.

Ganduje ya bayyana haka ne a yayin wata ziyara da manyan malaman jihar kusan 100 suka kai masa ranar Juma’a a gidan gwamnatin jihar.

Gidan talabijin na Channel TV ya ambato gwamnan na cewa ”Mun ba shi shawara ya dauki Musulmi a matsayin mataimaki kuma ya amince, saboda ba wani abu ba ne sabo a Najeriya”.

Ya kuma yi kira ga taron malaman da su rika yi wa Tinubu addu’o’in samun nasara a zaben 2023.

Related posts

Leave a Comment