Shugaban ?asa Bola Tinubu ya gana da jiga-jigan mambobin masu masana’antu da kuma wasu gwamnonin jihohi dangane da mawuyacin halin da tattalin arzikin Najeriya ya afka, gami da irin ra?a?in tsadar rayuwar da ake fama da shi a fa?in ?asar nan.
A ganawar wadda wasu gwamnoni suka halarta, sun tattauna matsalar yadda darajar Naira ta zube ?asa warwas, ita kuma Dalar Amurka sai ?ara yin sama ta ke yi.
Daga cikin wa?anda suka halarci taron a ?angaren hamsha?an masu masana’antu da manyan kamfanonin zuba jari, akwai:
Aliko ?angote, Abdulsamad Rabi’u mai BUA, Tony Elumelu mai Bankin UBA, Segun Ajayi-Kadir, Babban Daraktan ?ungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya (MAN).
A ?angaren gwamnoni kuma akwai na Ogun Dapo Abiodun, na Anambra, Charles Soludo a taron wanda aka yi a Fadar Shugaban ?asa, a ranar Lahadi.
Tinubu ya shaida wa hamsha?an cewa an shirya taron ne a dubi abin da gwamnati ke yi wanda shi ne daidai, sannan kuma a duba hanyoyin da za a bi domin a farfa?o da tattalin arzikin ?asa.
Premium Times ta ruwaito cewa Tinubu ya ce yayin da gwamnatin ba ta da dukkan la?ani da fahamin da za ta magance dukkan matsalolin, duk da haka za ta ci gaba da lalube, “har sai ta samar wa ?asar nan nagartaccen tsari da fasalin tattalin arziki wanda zai ?ora ta kan hanya madaidaiciya.”
“Kamar yadda na fa?i, nauyin da ke kan mu kawai shi ne mu da?a?a wa ‘yan Najeriya, ba ‘yan wata ?asa ba. To kuma mun damu sosai dangane da halin da kowa ke ciki, tun daga ?alibai, iyaye mata da iyaye maza, manoma, ‘yan kasuwa, ‘yan tireda. Mun fahimci dukkan mu dai duk daga cikin rijiya ?aya mu ke shan ruwa,” inji Tinubu.
“Muna ta laluben wasu hanyoyin da zamu bi domin taimakon talakawa da marasa galihu domin mu farfa?o da tattalin arzikin ?asa.”
Bayan fitowa daga taron, ?angote, Abdulsamad da Elumelu sun yi wa manema labarai ?arin haske.
“Ina ganin mun yi ganawa mai amfani sosai, kuma wadda za ta yi tasiri matu?a. Kuma abubuwan da muka tattauna duk sun dangane matsalar tattalin arzikin ?asa, matsalar abinci, sai kuma matsalar tsaro da suka addabi ?asar nan a yanzu. Kuma mun tattauna kowace matsala dalla-dalla,” cewar ?angote.
“To akwai Kwamitin Mashawartan Shugaban ?asa Kan Tattalin Arziki, wanda Shugaban ?asa ya kafa. To wannan kwamiti ne zai duba dukkan batutuwan da muka tattauna domin magance su.
“Kama tun daga samar wa mutane aiki, magance matsalar tsadar abinci da sauran batutuwan da suka shafi tattalin arzikin ?asa.”
“To duk mun tattauna wa?annan batutuwan dalla-dalla. Ba zan iya ba ku bayanin dukkan abubuwan da muka tattauna ba a yanzu, amma dai muka kyautata zato tare da ya?inin cewa muna da ?asaitacciyar ?asa. Muna da dukkan abin da muke bu?ata domin farfa?o da tattalin arzikin mu, kuma za mu yi haka ?in.”
A na sa ?arin bayanin, Abdulsamad Rabi’u ya ce fa?uwar darajar Naira ba ?ayyadajjen abu ba ne. Ya jinjina wa Babban Bankin Najeriya (CBN), dangane da ?o?arin da ya ke yi wajen saisaita matsalar.
“Mun tattauna yadda za mu rage tsadar canjin Naira da ku?a?en waje. Saboda abin da ke faruwa dangane da canji, ?ir?irarre ne. Amma mun gode Allah Babban Bankin Najeriya, CBN ya na bakin ?o?arin sa matu?a,” inji shi.
“Yanzu dai Dala ta ?an sauko daga N1,800 zuwa har N1,500. To kuma kun san dai komai na ?asar nan sai da ku?a?en waje, in dai ana maganar kayan da ake shigo da su ne cikin ?asar nan.”
