Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa yayin da hauhawar farashin kayayyaki ke ?ara tsananta, a ranar Laraba, 6 ga watan Maris, majalisar wakilai ta yi kira da a biya ma’aikatan Najeriya albashi mai kyau.
Majalisar ta kuma umarci kwamitocin kwadago da samar da ayyuka, ku?i da tsare-tsare da su tsara hanyoyin biyan albashin ma’aikatan Najeriya a farashin da ya yi daidai da yanayin tattalin arzi?in da ake ciki.
Da yake jagorantar muhawara kan ?udirin, mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Aliyu Madaki, ya ce hauhawar farashin kayayyaki a ?asar nan ya sa talakawan Najeriya cikin wahala. Ya yi nuni da cewa biyan bu?atun yau da kullum da suka ha?a da abinci, ruwa, gidaje, ilimi, kiwon lafiya, sufuri, tufafi, da sauransu na neman gagarar ?an Najeriya.
A cewarsa: “Hauhawar farashin kayayyaki a ?asar nan ya yi mummunan tasiri a kan tsadar rayuwa, inda farashin abinci, wurin kwana, ilimi, da sufuri ya yi tashin gwauron zabi.” Duba da yanayin tattalin arzi?in da ?asar nan ke ciki, majalisar ta yi nuni da cewa babu wani ma’aikaci da zai iya rayuwa a Najeriya da albashi ?asa da N100,000 a kowane wata.
