?aramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya ce makaho ne ka?ai zai iya cewa Bola Ahmed Tinubu ya gaza a mulkin da ya fara.
Matawalle ya caccaki ?ungiyar Dattawan Arewa NEF a Karkashin Jagoran Profesor Ango Abdullahi kan barazanar da ta yi cewa Arewa za ta sauya shugaba Tinubu a 2027
Tsohon gwamnan ya ce Tinubu ya shirya yi wa Arewa ayyuka masu yawa kuma NEF ba ta da ikon yanke hukuncin wanda ?an Arewa za su za?a
Duk wanda ke kallon Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya gaza ko mai rauni, ko dai makaho ne ko ?ataccen da ya kasa ganin sabuwar Najeriyar da ta kunno kai.
Kungiyar dattawan Arewa ta bakin mai magana da yawunta, Abdul-Azeez Suleiman ta nuna nadamar yadda yankin ya zabi Tinubu a 2023.
Kungiyar ta ?ara da cewa daga yanzu, Arewa za ta fi maida hankali kan ha?a kai wuri ?aya da maslaha wajen za?en ?an takarar kujera lamba ?aya a Najeriya.
Amma tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana ?ungiyar a matsayin “nauyin siyasa”, inda ya dage cewa NEF ba ita ba ce, kuma ba za ta taba zama mai magana da yawun Arewa ba. Matawalle ya ce shi da sauran su sune manyan jagororin Arewa ba za su tsaya su zuba ido wasu ‘tsirarun mutane’ sun ?ata wa yankin Arewa suna ba.
“Duk wanda ke kallon Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya gaza ko mai rauni, ko dai makaho ne ko ?ataccen da ya kasa ganin sabuwar Najeriyar da ta kunno kai”.
Matawalle ya ce duk mai hankali ya ga ayyukan da Tinubu ya ?auko yi a Najeriya
Neman suna kawai ?ungiyar dattawan Arewa (NEF) ke yi – Amman Gaskiyar magana Shugaba Tinubu na son yankin Arewa kamar ransa -inji ?aramin ministan tsaro bello Matawalle
