Tinubu Ya Yi Azarbabi Wajen Janye Tallafin Mai – Atiku

Labarin dake shigo mana daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Tsohon mataimakin shugaban ?asa Atiku Abubakar ya soki matakin shugaba Bola Tinubu na cire tallafin mai ba tare da samar da hanyoyin sau?a?a wa al’umma ba inda ya ce an ?auki matakin ba tare da yin zuzzurfan nazari ba.

Atiku Abubakar wanda shi ne ?an takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban ?asar da ya gudana, ya yi wannan suka ne a wani taron PDP da aka shirya wa za?a??un jami’ai a jihar Bauchi.

A cewar Atiku, “tsakanin 1999 da 2007, gwamnatin PDP ta ?ullo da batun cire tallafin mai kuma ni na jagoranci kwamitin. Mun cimma ?udirin ta hanyoyi biyu amma sai bayan samar da kayayyakin rage ra?a?in matakin ga wa?anda lamarin ya shafa,”

“Mun ?an?ana irin wannan a matsayin jam’iyya da ke mulki. Da abin da za mu yi ke nan ba wai kawai sanar da janye tallafi ba, ba tare da tattaunawa da ?angarorin da abin ya shafa ba.” in ji Atiku Abubakar.

Bola Tinubu dai ya bayyana matakin janye tallafin man a lokacin da yake jawabinsa na farko ga al’ummar Najeriya bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ?asa.

Kuma tun lokacin ne al’ummar ?asar suka shiga ru?ani kasancewar farashin mai ya tashi ga kuma hauhawar farashin kayayyaki.

Related posts

Leave a Comment