Mai Martaba Sarkin Birnin Gwari Malam Zubairu Jibril Mai Gwari II ya ce zuwa yanzu sun ga amfanin matakan da gwamnatin jihar Kaduna ke ?auka da zummar da?ile ayyukan ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane.
Zubairu Jibril Mai Gwari II ya bayyana cewa matakan sun takure ‘yan bindigar, abin da ya sa yanzu suke neman abinci daga wajen mutanen da suka sace maimakon ku?in fansa.
Sarkin ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin taron ?addamar da rahoto kan matsalar tsaro da Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta jihar ta gabatar wa Gwamna Nasir El-Rufai.
“Mun nuna cewa matakan da gwamnati ta ?auka na toshe layukan salula da hana hawan mashin da hana sayar da man fetur a ko’ina ya yi amfani ?warai da gaske domin mun gani a wajenmu kuma muna da labarin sauran wurare,” in ji shi.
“Wa?annan matakai sun takura su ta yadda idan suka saci mutane sai dai su ce a ba su abinci ba ku?i ba. Muna goyon bayan gwamnati kuma muna addu’ar Allah ya kawo ?arshen wannan abu.”
Rahoton ya duba rikice-rikicen da suka faru na ‘yan fashin daji da ?abilanci daga 1 ga watan Yuli zuwa 30 ga Satumban 2021.
Mutum 343 aka kashe sannan aka saci 830 tare da jikkata 210 jumilla sakamakon tashe-tashen hankalin.
