Shugaban ?asa Bola Tinubu ya isa birnin Riyadh na Saudiyya don halartar taron Tattalin Arziki na Musamman na Duniya da za agudanar a ?asar.
Taron zai mayar da hankali wajen ha?in kai don bun?asa samar da makamashi a duniya.
Shugabannin gwamnatoci da na cibiyoyin kasuwanci da masana fiye da 1,000 ne daga ?asashe 90 ake sa ran za su halarci taron da za a gudanar a birnin Riyadh.
Manufar taron ita ce ?ora wa kan nasarorin da ka cimma a taron shekarar da ta gabata da aka gudanar birnin Geneva na ?asar Switzerland.
Mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Ajuri Ngelale ya ce ya ce shugaba Tinubu zai yi amfani da taron wajen ?arfafa manufofin gwamnatinsa da ake yi wa la?abi da “Renewed Hope Agenda”.
Tun da farko shugaba Tinubu na ziyarar aiki a birnin Hague na ?asar Netherlands, bisa gayyatar da firaminstan ?asar ya yi masa don wata tattauna hanyoyin zuba jari tsakanin ?asashen biyu.
