Ministan Harkokin Ku?a?e Wale Edun, ya ce Najeriya ta ci jarabawar cancantar kar?ar lamunin Dala biliyan 2.25 daga Bankin Duniya.
Edun ya bayyana haka yayin wata ganawa da manema labarai, wadda Ma’aikatar Harkokin Ku?a?e da Babban Bankin Najeriya (CBN) suka shirya ta ha?in-gwiwa.
Sun shirya ganawa da manema labarai ?in lokacin da suke halartar taron Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF), a birnin Washington, D.C, Amurka.
Idan aka kar?o bashin za a tsunduma ku?a?en wajen ayyukan bun?asa tattalin arzikin ?asa, yayin da ake fama da wannan gaganiyar ?alubalen tsadar rayuwa a fa?in Najeriya.
Bankin Duniya ya na bai wa ?asashe lamuni wanda babu ku?in ruwa ko kuma mai ku?in ruwa wanda bai wuce kashi 1% bisa 100% ba, domin su farfa?o ko bun?asa tattalin arzikin su.
Minista Edun ya ce lamunin babu takurawa a cikin yarjejeniyar kar?ar sa, domin sai nan da shekaru 40 za a biya shi. Kuma kashi 1% bisa 100 ne kacal ku?in ruwan sa.
