Taron Bunkasa Tattalin Arzikin Matasa Da Tsaro Zai Dawo Da Kimar Taraba – Benjamin Bako

BASHIR ADAMU, JALINGO.

A karon farko, Gwamnatin Jihar Taraba ta kafa Kwamitin bunkasa tattalin arzikin Matasa da tsaron Jiha Karkashin jagorancin Mr. Benjamin Bako. Inda suka shirya taron koyama Matasa Sana’o’i, tare da baiwa masu bukatar sanya jari a Jihar tabbacin tsaro a Jalingo fadan Jiha.

Da yake jawabi a lokacin bude taron, Shugaban Kwamitin Mr. Benjamin Bako yace ko shakka babu taron zai dawo da kimar Jihar Taraba a idon Duniya.

Bako ya kara da cewa ya zama wajibi Al’ummar Jihar Taraba baki daya su sauya zukatansu, domin samun nasaran sabuwar Gwamnatin da Dr. Kefas Agbu ke jagoranta, a yayin da suke kokari wurin ganawa da gayyato masu saka jari Jihar ta Taraba.

A cewar Benjamin “Talauci na da matukar tasiri wurin janyo rashin tsaro a Kasa, a saboda haka dole ne suyi tsayin daka wurin koyama Matasan Jihar Taraba yanda zasu iya kama Kifi, ba wai mu rinka kama kifi muna basu ba.

“A yanzu haka mun daura tubalin koyama Matasa sanao’in hannu, kuma matasan sun fitone daga dukkanin Kananan Hukumomi goma sha shida (16) dake fadin Jihar Taraba.

“A madadin sabon Gwamnan Jihar Taraba, Dakta Kefas Agbu, ina mai tabbatar muku cewa; ya daura aniyar sauya akalan Jihar, ta inda Al’ummar ta zasuyi dogaro da kansu, suyi tafiya da kafafunsu, ba tare da dogaro da albashin gwamnati kawai ba.

“Zamu tabbatar da koyama Matasan mu, ilimi da fasahar kimiyya na zamani ta inda za suyi gogayya da sauran Matasa a Duniya ta hanyar dogaro da kai.

Related posts

Leave a Comment