Taraba: Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Jam’iyyar APC

BASHIR ADAMU, JALINGO

Wani sabon rikici ya barke a Jam’iyyar APC Jihar Taraba sakamakon sauya zababbun Shugabannin Kananan Hukumomi guda hudu.

A ranar Asabar ne Jam’iyyar APC ta sake rantsar da wasu sabbin Shuwagabanni Kananan Hukumomin Ussa, Wukari, Ibi da Takum.

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Taraba, Ibrahim Tukur El-sudi ne ya jagoranci rantsarwan, inda wasu bayanai ke cewa yayi hakan ne bisa umurnin Uwar Jam’iyyar ta Kasa da ta turo mishi da sunayen wadannan sabbin Shugabanni hudu.

Inda yace wadannan zababbun Shugabannin da aka sauya, su daina bayyana kansu da Shugabannin Jam’iyyar domin an riga an ciresu, duk da cewa ba’a bayyana laifin da suka yi aka ciresu ba.

Sai dai kuma a wani mataki na maida martani dangane da matakin na El-sudi, Kungiyar Yakin neman Zaben Gwamnan Jihar Taraba na David Sabo Kente, sun shaidawa Shalkwatan Jam’iyyar APC na Kasa da su gaggauta wannan yunkurin canjin Shugabannin da sukayi batare da wani laifi ba, ko kuma su kalubalanci matakin a Kotu, kamar yanda shugaban Kungiyar, Abba Akawu- Zaga ya aiyana yayin ganawanshi da Yan-Jaridu a Ranar Lahadi.

” An kori Shugabannin Jam’iyya na Kananan Hukumomi hudu, babu gaira babu dalili wadan da akazabesu tare da Shuwagabannin zartarwar Jiha, toh ku sani wadanda aka rantsar a ‘jiya’ ba zababbu bane, kuma bamu san suba, kuma Kundin tsarin malkin Jam’iyya bai san da suba a hukumance, hakan yin karan tsaye ne ga Jam’iyyan da ba zai haifar da ?a mai ido ba.

Akawu- Zaga ya ankarar da Jam’iyyar cewa dole su tuna da hadarur-rukan dake tattare da rashin samun nasaran Jam’iyyar a zaben da ya gabata na Shekara ta 2019 dakuma na 2023 dake tafe.

Related posts

Leave a Comment