Labarin dake shigo mana daga Jihar Gombe na bayyana cewar biyo bayan kisan da akayi wa wata ?aliba mai suna Deborah a kwalejin ilimi na Shehu Shagari a jihar Sokoto bisa zargin batanci ga Annabi Muhammad SAW.
Rundunar ‘yan Sanda a Gombe ta gudanar da tattaki inda jami’an rundunar a cikin Motoci dauke da manyan makamai suka rin?a zagaye cikin anguwannin da Majami’u don tabbatar da cewa abubuwa na tafiya lafiya.
Da yake ?arin haske akan tattakin kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Gombe ASP Mu’azu Abubakar yace an yi tattakin ne domin tauna tsakuwa don aya taji tsoro, da kuma aikewa da sako ga ?ata gari gami da daukar matakai na dakile duk wani abu da ka iya tasowa a silar mutuwar daliba Deborah a Sokoto.
Mu’azu Abubakar ya ?ara da cewa tattakin ba wai sabon abu bane suna yin shi ne lokaci zuwa lokaci duk a kokarin ganin an dakile duk wani abu da zai iya zama barazana ga zaman lafiya a jihar Gombe.
