Talakawa Na Ji A Jikinsu Sosai – Sarkin Kano Ga Buhari

An bayyana cewar Talakawa a Najeriya na fama da matsala ta tsadar rayuwa da wahala sosai wanda ya dace shugabanni su duba lamarin nasu domin saukaka musu.

Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero yayi wannan kiran lokacin da yake mayar da jawabi a yayin ziyarar da mai girma Shugaban ?asa Buhari ya kai fadarshi dake birnin Kano.

Mai Martaban ya kuma bukaci jama’a da dagewa wajen gudanar da addu’o’i ga shugabanni da fatan samun sauki a ?asa.

Tun farko da yake jawabi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga Gwamnoni, dasu koyi dabi’ar Kammala ayyukan cigaba, domin su magance daukar tsawon lokaci ba aka Kammala ba, da Kuma kashe kudi, ba tare da tunanin wata Gwamnati ce ta gina aikin ba.

Mai Magana da Yawun Shugaban Kasar Malam Garba Shehu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa, inda yace Shugaban Kasa Buhari yayi wannan kiran ne a lokacin da yakai ziyarar ban girma ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a ranar Alhamis a Kano.

Shugaba Buhari Wanda ya yabawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje dayake ta gudanar da ayyukan cigaba, yace Kammala ayyukan da ya gada ga Gwamnatin data wuce, wata alama ce ta kyakkyawan Shugaban ci ga Gwamnan.

A lokacin da yake jaddada bukatar kirkirar irin wadannan ayyukan a cikin Al’umma, Buhari yace yaji dadi daya ga Gwamnan na kirkira tare da Kammala ayyukan cigaba.

Buhari yace yana farin ciki ganin yadda Gwamnan ya Kammala ayyukan daya gada daga tsohuwar Gwamnati.

“Ya nuna cewa Ganduje ba maketaci bane, Kuma ba makaryaci bane”inji shi.

Shugaban Kasa yace yana farin ciki ganin yadda Gwamnan yake gina wasu ayyuka, inda ya kara dacewa “wannan itace kadai hanyar daza’a nuna inda ake kashe kudaden Al’umma.”

A jawabin shi, Gwamna Ganduje ya bayyana godiyar Gwamnati da Al’ummar Jahar Kano ga irin kula, da Kuma soyayya da Shugaban Kasar ke nuna wa, musamman ta fuskar bayar da mukamai da ayyukan Gwamnatin Tarayya da ake shimfida wa a Jahar.

Yace ayyukan sun hada da Layin Dogo daga Kano zuwa Kaduna na Zamani, Wanda aikin ya fara a ranar 15 ga watan juli.

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yiwa Shugaban Kasa maraba da zuwa Masarautar sa, inda yace ta zama kamar gidan sa.

Ya godema Shugaban Kasa ga irin dimbin ayyukan cigaba daya keyi a Jahar, da Kuma fadin Kasa, duk da irin matsin tattalin arziki Wanda cutar Covid-19 ta janyo.

Related posts

Leave a Comment