Dillalan Raguna Sun Koka Akan Rashin Samun Ciniki

‘Yan kwanaki kadan kafin gudanar da bikin Babbar Sallah, dillalan ragunan layya sun fara koka rashin ciniki yadda ya kamata a birnin Zazzau da Kano da kuma garin Kaduna da sauran yankunan kasar.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), wanda ya ziyarci wasu kasuwannin raguna a sassa daban-daban a ranar Alhamis ya ruwaito cewa dillalan ragunan da dama sun koka da karancin ciniki.

Akwai adadi masu yawa na raguna a dukkan kasuwannin da aka ziyarta, inda dillalan ke jiran masu siye da jiran tsammani.

Kasuwannin da aka ziyarta sun hada da kasuwar shanu ta lpata, kasuwar raguna a babbar kasuwar nan ta Mandate, da kasuwar Adeta, da kasuwar raguna ta Ode Alfa-Nda, da kuma kasuwar raguna ta Zango.

Farashin na raguna sun yi kamanceceniya a kusan dukkanin kasuwanni kasancewar ana sayar da mafi kankanin rago tsakanin N35,000 zuwa N40,000 yayin da manyan ragunan suka kasance daga N100,000 zuwa N150,000.

Haruna ?an Kasim dillalin rago a kasuwar shanu ta Zango, a wata hira da NAN ya ce dillalan na fuskantar karancin ciniki duk da cewa Babbar Sallah saura ‘yan kwanaki.

Ya danganta lamarin da rashin kyakkyawan yanayin tattalin arziki a kasar. A cewar dillalin: “Zuwa yanzu ya kamata mun yi ciniki mai matukar yawa amma masu saye sukan zo jifa-jifa mutum daya ko biyu suna sayen daya yayin da wasu ba za su iya biyan farashin ba.”

Wani lauya kuma mai son siye rago, Sani Abdullahi ya ce bai sayi rago ba har yanzu saboda rashin wadatar kudade.

Related posts

Leave a Comment