Takarar Majalisa: Rarara Ya Yi Mini Shigo-Shigo Ba Zurfi – Alan Waka

Mawaki Aminu Alan Wa?a ya fice daga jam’iyyar ADP ta Sha’aban Ibrahim Shara?a, sannan ya yi wurgi da takarar majalisar tarayya da yake yi a ?aramar hukumar Nassarawa.

A cikin sa?on bidiyon da ya fitar, Ala ya nuna yayi danasanin fitowa ya bayyana kansa a matsayin ?an takarar, domin ya ce babu wata takardar shaidar cewa yana takara da ya gani.

Ya kuma zargi ?ungiyar 13×13 da mawa?i Dauda Kahutu Rarara ke jagoranta, wanda babban jigon ADP ne a Kano da yi musu angiza mai kantu ruwa kan shiga jami’yyar bisa shara?i.

Sai dai ya ce, daga baya ?ungiyar ta kasa yin kata?us domin sanar da su matsayarsu, kurum an barsu da magana da wadanda ba su da hurumi.

Ala ya ce, tuni ya aike wa jami’yyar takardar sallama.

Daga Freedom Radio

Related posts

Leave a Comment