Gwamnonin APC Na Tare Da Takarar Tinubu – Bagudu

Shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya yi watsi da ikirarin cewa wasu gwamnonin jam段yyar na tattaunawa da dan takarar shugaban kasa, jam段yyar PDP, Atiku Abubakar.

Bagudu ya ce Gwamnonin APC ba sa aiki da PDP a kan burin dan takarar shugaban kasa na jam段yya mai mulki, Bola Tinubu.

Ya bayyana hakan ne a yayin taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam段yyar APC a Kano .

Bagudu ya ba da tabbacin cewa gwamnonin APC na bayan burin Tinubu na zama shugaban kasa.

A cewar Bagudu: 泥ukkan gwamnoninmu suna goyon bayan takarar Tinubu.

的kirarin da wasu ke cewa wasu gwamnonin APC na tattaunawa da 惣an adawa karya ne. Dukkan gwamnoninmu suna goyon bayan takarar Tinubu
Kalaman na sa sun zo ne lokacin da Gwamna Nyesom Wike ya yi zargin cewa wasu gwamnonin APC na aiki da Atiku.

Related posts

Leave a Comment