Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru Ahmad El Rufa’i ya bayyana cewar ko shakka babu ta’addanci da ta’asar ‘yan Bindiga ta fi muni da yin kamari a ?arkashin mulkin Buhari tun bayan da Shugaban ya hau karagar mulki a shekarar 2015.
El Rufa’i ya bayyana hakan ne a yayin ganawar shi da Shugabannin hukumar SSS shiyyar Arewa maso yamma a Kaduna ranar Alhamis.
Gwamnan ya ?ara da cewar harkar tsaro ta yi matukar ta?ar?arewa a karkashin Mulkin Buhari idan aka kwatanta da gwamnatocin baya duk da bugun kirjin da ake yi na cewar an yi nasara akan Boko Haram.
“Abu ne wanda yake a fili kowa yana gani a baya can matsalar tsaron nan tana wani yanki guda ne amma a yanzu matsalar ta yi naso zuwa sassa daban daban na kasar musanman yankin Arewa inda ‘yan Bindiga ke cin Karen su ba babbaka a har kullum.
“Baya ga matsalolin da a baya ake samu a yankin Kudancin Kaduna, a yanzu an wayi gari kusan jihar gaba daya tana fuskantar barazanar ‘yan Ta’adda inda satar mutane da neman ku?in fansa ya zama ruwan dare”.
A bisa ga wata ?ididdiga da gwamnatin jihar ta fitar sama da mutane 300 ne aka kashe, yayin da aka yi garkuwa da sama da mutum 1000 a tsakanin watan Janairu zuwa Afrilu na shekarar 2021 a jihar Kaduna kadai.
