Ta’addanci Zai Zama Tarihi A Jihar Borno – Zulum

Rahotanni daga birnin Maiduguri na bayyana cewar Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno ya bayyana cewa da izinin Allah za’a kawo karshen ayyukan ta’addaci da ya addabi mutanen jihar zuwa shekara mai kamawa 2022.

Gwamna Zulum ya fa?i wannan magana ne yayin da yakai ziyara garin Monguno domin duba yadda aikin gina babban asibitin garin ke tafiya.

Hare-haren yan ta’addan ?ungiyar Boko Haram ya lakume rayukan dubban mutane da kuma tilastawa wasu guduwa domin tsira da rayuwarsu a cikin shekaru 12.

A ziyarar bazata da ya kai Gwamnan ya tarar da wasu ma’aikatan lafiya ba su zo aiki ba a ranar Laraba da yakai ziyarar, kuma cikin gaggawa ya ?auki matakan da suka dace.

Ba tare da ?ata lokaci ba Zulum ya bada umarnin dakatar da albashin wa?anda sukanyi fashi sannan ya bada umarnin karin albashi ga wa?anda suke zuwa aiki nan take.

A jawabin da yayi a asibitin Zulum yace: ““Duk ma’aikatan lafiyan da suka cancanta za su samu karin kashi na albashinsu daga yanzu zuwa shekara daya mai zuwa, lokacin da ake sa ran ta’addanci ya kau.”

Gwamna Zulum ya kuma ?auki alkawarin cewa gwamnatinsa zata kara ?aukar sabbin ma’aikatan lafiya a asibitin na garin Monguno. Hakazalika Zulum ya yi al?awarin gina sabbin gidaje 15 wa?anda za’a baiwa ma’aikatan su ji da?in aikinsu yadda ya kamata.

A ?angarensa, shugaban asibitin Monguno, Isa Akinbode, ya koka wa Zulum cewa suna fuskantar karancin ma’aikata da rashin dakin gwaje-gwaje a asibitin.

Related posts

Leave a Comment