Gwamnatin Sudan ta ce za ta mika tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir ga kotun hukunta laifukan yaki ta duniya wato International Criminal Court.
Ministan harkokin wajen kasar Mariam al-Mahdi, wanda ya tabbatar da hakan ranar Laraba, ya kara da cewa za a gurfanar da hambararren shugaban kasar ne tare da jami’an gwamnatinsa bisa rikicin da ya faru a yankin Darfur.
Kafofin watsa labaran kasar sun ambato Mahdi yana cewa “majalisar ministoci ta yanke shararar mika jami’an gwamnatin da kotun ICC take nema ruwa a jallo.”
Bashir, wanda ya kwashe fiye da shekara 30 yana mulkin kasar amma aka hambarar da shi a 2019, yana fuskantar zarge-zargen laifukan yaki da na cin zarafin bil adama sakamakon rikicin Darfur.
