Sukar Buhari: Da Yiwuwar Mu Hukunta Tinubu – APC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban jam’iyyar APC na ?asa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce da yiwuwar jam’iyyar ta hukunta Asiwaju Bola Tinubu kan kalaman da ya yi akan shugaban ?asa Buhari.

A lokacin da ya ziyarci Abeokuta, birnin jihar Ogun, a ranar Laraba, Tinubu ya shaida wa wakilan jam’iyyar APC cewa ba don shi ba, da Buhari bai zama shugaban kasa a 2015 ba.

Wannan tsokaci dai ya janyo cece-kuce a fadin kasar nan.

Da ya ke zantawa da manema labarai a shelkwatar jam’iyyar APC da ke Abuja a ranar Asabar, Adamu ya ce, “Muna iya hukunta shi (Tinubu) kan kalaman da ya yi akan Shugaban kasa.”

Adamu ya kuma ce babu wani dan takarar shugaban kasa da aka haramtawa tsayawa takara a zaben fidda-gwani na shugaban kasa na jam’iyyar da ake shirin yi a ranar Litinin.

Related posts

Leave a Comment