Hukumar yaki da masu safarar miyagun kwayoyi ta ?asa NDLEA, ta shafa fenti a jikin wasu gidaje shida da wani katafaren gini mai shaguna a Maiduguri mallakin jami’in dan sanda DCP Abba Kyari.
Katafaren ginin bene ne mai hawa biyu mai suna Assurance Plaza da ke kan titin barikin Giwa a Maiduguri kuma yana da shaguna 100.
Baya ga ginin, hukumar na kuma binciken wasu gidajen zama shida a cikin unguwar masu hannu da shuni ta New GRA Maiduguri.
