Siyasar Kano: Rimin Gado Ya Sauya Sheka Zuwa PDP

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Muhyi Rimin-Gado, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP gabannin zaben 2023.

Rimin-Gado ya bayyana cewa ya mika takardar neman shiga PDP ta yanar gizo yayin da yake sa ran yin rijista a unguwarsa ta karamar hukumar Rimingado a watan Fabrairu mai kamawa.

Tun bayan dakatar da shi da gwamnatin jihar Kano ta yi a ranar 5 ga watan Yulin 2021, fastocin tsohon shugaban na hukumar yaki da cin hanci sun karade unguwanni a Kano inda suke ayyana aniyarsa na takarar gwamna a zabe mai zuwa.

Yayin da wasu daga cikin fastocin suka bayyana babu tambarin kowace jam’iyya, sauran na dauke da tambarin APC.

Sai dai kuma, Magaji ya kauracewa harkokin APC a matakin karamar hukuma da jiha kuma bai hade da kowani bangare ba na tsagin jam’iyyar mai mulki.

Idan ba a mance ba a watan Disamban 2021, yan sanda sun dakile wani yunkuri na Rimin-Gado don yin jawabi ga dubban matasa a Kano domin tunawa da ranar yaki da rashawa ta duniya inda suka rufe wajen taron.

Sai dai kuma, da yake magana kan dalilinsa na komawa PDP, Rimingado ya ce ya shiga jam’iyyar adawar ne saboda ita kadai ce za ta ceto jihar Kano daga rikicin siyasar da take ciki a yanzu.

Related posts

Leave a Comment