GUGUWAR MAILANTARKI: Mataimakin Shugaban PDP Gombe Ta Tsakiya Ya Koma NNPP

Farin jinin ?an takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyyar NNPP, Khamisu Mailantarki na ci gaba da yin tasiri a jihar, ta yadda shugabannin manyan jam’iyyu da mambobin su ke ci gaba da kwarara cikin NNPP.

Na baya-bayan nan nan dai su ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Shiyyar Gombe ta Tsakiya, Injiniya Musa Gwani (Bimason) da Mataimakin Ma’ajin PDP na jiha, Muhammad Yusuf (Malam Pindiga) ne su ka koma NNPP.

A cikin wani faifan muryoyin da su ka ya?a na dalilin ficewar su, wanda tuni wakilin mu ya samu muryoyin na su, sun bayyana cewa NNPP ce mafita ga al’ummar Gombawa a za?en 2023.

Tuni dai PDP da APC mai mulkin Gombe ke ci gaba da rasa mambobin ta da shugabannin ta masu ficewa su na komawa NNPP.

Hakan kuwa tuni ya maida NNPP ta zama babbar jam’iyyar adawa a Jihar Gombe.

Jin?ai Da Agaji:

A wata sabuwa kuma, Mailantarki ya bayar da gudummawa naira milyan 2.2 ga iyalan wa?anda ‘yan bindiga su ka kai wa farmaki a garuruwan Amtawalan da Paboure da ke ?ar?ashin gundumar masarautar ?aramar Hukumar ?illiri.

Ya bayar da tallafin ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje da ta’aziyya ga iyalan ?auyukan guda biyu, a ranar Asabar.

Dangane da masu tururuwa zuwa cikin NNPP kuma, idan ba a manta ba cikin makon jiya ne Mailantarki ya kwashe baraden ya?in Isyaku Gwamna, daga PDP su ka koma cikin rundunar NNPP.

A cikin wancan labarin, ?an takarar gwamnan Jihar Gombe a jam’iyyar NNPP, Khamisu Ahmed Mailantarki, ya na ci gaba da kar?ar dandazon manya da ?ananan magoya bayan APC mai mulkin jihar da kuma PDP.

A ?arshen makon nan ne Mailantarki ya haska wa wasu manyan mambobin PDP hanya, su ka bi ta gwadaben da su ka koma NNPP.

Mambobin dai zaratan magoya bayan fitaccen ?an siyasar nan ne Jamil Isyaku Gwamna, wa?anda ake kiran ?ungiyar su da suna Sardauna Dawo-Dawo.

A ranar Juma’a ce Mailantarki ya kar?i dandazon ‘yan PDP ?in a bisa tarbar su da Shugaban NNPP na Jihar Gombe ya yi, wato Alhaji Abdulahi Maikano.

Wannan dandazon magoya baya dai sun canja sunan su daga Sardauna Dawo-Dawo zuwa Mailantarki Movement, bayan sauya she?ar su daga PDP zuwa NNPP.

Sun bayyana cewa sun yanke shawarar goyon bayan ?an takarar da “matashi ne mai jini a jika, wanda ke da jama’a a kowane ?angaren al’umma, nagari na kowa, ?wararre, kuma mai zuciyar tausayin al’umma.”

Shugaban tawagar mai suna Muhammad Makson ya bayyana cewa Gombawa ba su da wata matsala da Mailantarki, domin an jaraba shi a baya, kuma ya ci jarabawar ri?on amanar da aka dam?a masa.

“A kan haka, Mailantarki na da gogewar da zai iya magancewa da shawo kan matsalolin da su ka dabaibaye jihar Gombe.

“Gaba ?ayan mu ne mu ka yi shawarar ficewa daga PDP mu ka yanke shawarar dawowa cikin NNPP, saboda bu?atar ganin mun samu nagartaccen shugabancin da ya fi dacewa da Jihar Gombe.

“Mun yi amanna cewa Mailantarki ne zai iya tsamo Jihar Gombe daga kwazazzabon ramin da APC ta jefa jihar, sakamakon tu?in gangancin da ake yi da motar da APC ta cika da lodin al’ummar Gombe.”

Makson ya ce wa?anda su ka fice daga PDP ?in zuwa NNPP akwai shugabanni 2000, mambobi sama da 20,000 a fa?in maza?u 114 na Jihar Gombe.

Mailantarki ya tabbatar masu da cewa shi da NNPP za su tafi tare da su domin a gudu tare, a yi nasarar kafa gwamnati tare.

Daga nan ya ro?esu cewa sai sun ?ara tashi tsaye sosai wajen ya?a manufofin NNPP da tallata ‘yan takarar jam’iyyar a cikin yankunan karkara, ta yadda za a kawar da gwamnatin APC a ranar za?en 2023.

Related posts

Leave a Comment