Shugabancin Najeriya Ya Fi Karfin Yaro – Tinubu

Rahotannin dake shigo mana daga Ibadan babban birnin Jihar Oyo na bayyana cewar tsohon gwamnan Jihar Legas kuma jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya fa?awa matasan ?asar cewa za su yi shugabancin ?asa amma sai bayan ya yi.

Fitaccen ?an siyasar ya fa?i haka ne a ziyarar da ya kai wa Alaafin na Oyo Lamidi Adeyemi, a ranar Lahadi.

Tinubu ya bu?aci matasa su ba magabatansu dama.

“Kun toshe wa magabatanku dama tun kafin ku zama shugaban ?asa, idan kun zama shugaban ?asa fa, za ku kore mu ne a gari?”

“Sai kun tsufa za ku zama shugaban ?asa, kuma sai na riga zama shugaban ?asa,” in ji Tinubu.

Matasa a Najeriya sun da?e suna fafutikar ganin sun kai ga madafan iko, da samun mu?aman siyasa.

Related posts

Leave a Comment