Ketare: Sarauniyar Ingila Ta Harbu Da Korona

Rahotanni daga fadar Sarauniyar Ingila dake birnin Landan na nuna cewa Sarauniyar Ingila, Elizabeth II mai shekaru 95 a duniya, ta kamu da annobar korona, kamar yadda rahoton Aljazeera ya bayyana.

Fadar masarautar Buckingham ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 20 ga watan Fabrairu shekarar 2022.

A cewar fadar, Sarauniyar na fama da alamun sanyi amma kuma za ta ci gaba da gudanar da harkoki kadan-kadan a Windsor a mako mai zuwa.

“Za ta ci gaba da samun kulawar likitoci sannan za ta bi dukkan matakan da suka dace.” Sarauniyar ta hadu da babban danta kuma yarima mai jiran gado, Yarima Charles wanda ya kamu da korona a makon da ya gabata.

Related posts

Leave a Comment