Shugabancin Majalisa: Tinubu Da Shettima Ne Suka Kayar Dani Ba Akpabio Ba – Yari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon Gwamnan jihar Zamfara Sanata Abdulazeez Yari Yace taron dangi da aka yi masa ne yasa ya fadi zaben shugabancin majalisar dattawan Najeriya.

Ya bayyana cewar Shugaban ?asa Tìnubu da mataimakinsa da gwamnoni ne suka dunkule wuri guda suka yake shi da tabbatar da cewa bai kai labari ba.

“Tun farko cancanta ta sa na tsaya takarar domin bada tawa gudummuwar wajen ciyar da ?asa gaba, kuma a matsayina na musulmi na amince da kayen da nasha.

Yari ya fadi hakanne a wata hira da muryar Amurka kan abinda yake ganin yasa baiyi nasara ba.

Related posts

Leave a Comment