An Roki Kamfanonin Jiragen Sama Su Janye Aniyar Dakatar Da Aiki

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin ta ro?i kamfanonin jiragen sama da kada su dakatar da aiki kamar yadda suka yi barazana daga Litinin ?in nan.

An ruwaito wata sanarwa daga ofishin Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika na cewa hakan zai yi tasiri kan tattalin arzi?in ?asa “wanda da ma yake a ?untace”.

Ministan ya bayyana damuwarsa kan “wahalhalun da kamfanonin ke fuskanta wajen samun man jirgin” amma ya ce ma’aikatarsa ba za ta iya yin wani abu ba.

“Abin damuwar shi ne samar da man jirgi ba a ?ar?ashin ma’aikatarmu yake ba, saboda haka iya abin da za ta iya yi shi ne a tattauna da hukumomi da mahukuntan da za su iya sama wa kamfanonin sau?i. Tuni aka fara aiwatar da hakan ?ar?ashin minista,” in ji shi.

Related posts

Leave a Comment