Shugabancin ECOWAS: Zan Tabbatar Da Tsaro Da Wanzuwar Dimokuradiyya A Afirka – Tinubu

Kamar dai yadda aka saba, bayan za?en duk wani shugaba a kowanne mataki, shugaban zai tashi ya yi godiya ya kuma bayyana al?awuran da zai cika a yayin jagorancinsa.

Irin haka ce ta faru ga shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu bayan za?ar da aka yi masa a matsayin sabon shugaban ?ungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, Ecowas.

Kakakin Shugaban Najeriya Abdul’aziz Abdul’aziz ya yi wa BBC ?arin bayani game da za?en Tinubu da kuma bayanan da ya gabatar bayan za?en nasa.

“?imar Najeriya na ?ara bun?asa a idanun ?asashen Afrika da Duniya baki ?aya, kuma wannan dalili ya sa suka bai wa Shugana Bola Ahmed Tinubu jagorancin wannan ?ungiya.

“Ka tuna bai yi wata biyu ba cikakku kan mulki amma darajar ?asar da kuma shi kansa ta sa suka ba shi jagorancin,” in ji Abdul’aziz.

Tinubu ya zayyana abubuwa uku da zai bai wa muhimmanci wa?anda suka ha?a da:

Tsaro da zaman lafiya

Duk da cewa abu ne sananne cewa yankin ?asashen da suka ha?a ?ungiyar na fama da matsalar tsaro amma Tinubu ya jadada bu?atar kawo ?arshen matsalar saboda muhimmancin da take da shi.

“Game da zaman lafiya da tsaro, barazanar takai matakin ?ololuwa da ya zama wajibi a ?auki matakan gaggawa domin shawo kan ?alubalen,” in ji sabon shugaban.

“Babu shakka ?arancin zaman lafiya a yankunanmu zai ci gaba da da?ile ci gabanmu, kuma yankin mu ya ci gaba da zama a baya.

A wannan ga?a, dole mu nuna damuwa da ci gaba da amfani da tsare-tsaren da muka kawo domin ganin ?arshen matsalar tsaro,”

Matsalolin ?ungiyoyin masu ?auke da makamai irinsu, Boko Haram da ISWAP ko shakka babu na haifar da koma baya a ci gaban yankin, in ji Tinubu.

A cewarsa matsalar na ?ara fa?a?a zuwa ?asashe da yankunan da a baya ba su fuskantarta.

Tabbatar da dimokra?iyya

Wannan maudu’i na ?aya daga cikin batutuwan da suka mamaye taron da ECOWAS ta gudanar karo na 63 a Guinea Bissau.

Saboda wasu daga cikin mambobin ?ungiyar ba sa ?an turbar dimokradiyya, ba da gangan ba, sai domin sun fa?a hannun sojojin juyin mulki.

?asashen Mali da Burkina Faso da kuma Guinea wa?anda mambobin ?ungiyar ne dukkansu sojoji ke jagorantarsu a yanzu.

Da wannan dama da ya samu Bola Tinubu na son amfani da hanyoyin shiga tsakani domin samun damar mayar da su turbar dimokra?iyya.

Za a yi wannan ne ta hanyar tabbatar da gudanar da za?uka, ta yadda fararen fula za su za?i shugabannin da za su jagorance su kan tafarkin siyasa.

Abdul’aziz ya ce “so yake ya tabbatar da an daina samun juyin mulki tsakanin sojoji, tsarin dimokra?iyya na daga wa?anda ake so a tabbatar, a bai wa mutane damar kawar da mutanen da ba su yi musu ba a matsayin jagorori.”

Ku?in bai ?aya

Abdul’aziz ya ?ara da cewa Tinubu ya yi tsokaci kan ku?a?en bai ?aya da aka jima ana maganarsu, wa?anda ko shakka babu samar da su zai ha??aka kasuwanci tsakanin ?asahen yankin.

Samar da ?u?in zai taimaka wajen sau?a?a wahalhalun kasuwanci da ke tsakanin ?asashen da duka mambobin wannan ?ungiya ne.

Kazalika zai sau?a?a wahalhalun da ake fuskanta wajen musayar ku?in ?asashen waje marasa tabbas da kuma fa?uwar darajar ku?a?en cikin gidan ?asahen ECOWAS.

A 2020 ne wasu daga cikin ?asashen ECOWAS suka amince su fara amfani da ku?in Eco na bai-?aya.

Sai dai gwamnatin Najeriya a lokacin ta bukaci a jinkirta kaddamar da kudin na bai daya.

Tana cewa saboda akasarin ?asashen ba su cika ka’idojin da aka gindaya ba wanda ta ce akwai bukatar a ?age lokacin kaddamar da ku?in.

Yanzu dai sabon shugaban ya yi maganar ku?in a wannan lokaci wata?ila ko ya gamsu da cewa lokacin samar da ku?in ya yi.

Za?en Shugaba Tinubu bai zo da mamaki ba, ganin cewa shi ne shugaban Najeriya na takwas da ya jagoranci wannan ?ungiya.

?ungiyar ECOWAS dai na da mambobi 15 da suka ha?a da Benin da Burkina Faso, da Cape Verde, sai kuma Gambia

Sauran su ne Ghana da Guinea da Guinea-Bissau da Ivory Coast da Liberia da Mali da Nijar da Najeriya da Senegal da Saliyo da kuma Togo.

Related posts

Leave a Comment