Shugaban ‘Yan Sanda Ya Bada Umarnin Nada Kwamishinoni A Jihohi 13

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sifeto Janar na yan sanda, Usman Baba Alkali, ya bada umurnin nada sabbin kwamishanonin yan sanda na jihohi 13, da birnin tarayya Abuja.

Kakakin hukumar, Frank Mba, a jawabin da ya saki ta shafin hukumar ta Facebook ranar Juma’a, 6 ga agusta, ya yi bayanin cewa an yi wannan sauyi ne domin kawo inganci ga tsaro.

Frank Mba yace jihohin da aka nada sabbin kwamishanoni sune: 1. Jihar Niger , CP Monday Bala Kuryas 2. Jihar Kwara, CP Emienbo Tuesday Assayamo 3. Jihar Nasarawa, CP Soyemi Musbau Adesina 4. Jihar Taraba , CP Abimbola Shokoya 5. Jihar Benue, CP Akingbola Olatunji 6. FCT Abuja, CP Babaji Sunday 7. Jihar Kogi, CP Arungwa Nwazue Udo 8. Jihar Kaduna, CP Abdullahi Mudashiru 9. Jihar Jigawa, CP Aliyu Sale Tafida 10. Jihar Enugu, CP Abubakar Lawal 11. Jihar Cross River, CP Alhassan Aminu 12. Jihar Bayelsa, CP Echeng Eworo Echeng 13. Jihar Kebbi, CP Musa Baba

Related posts

Leave a Comment