Za A Yi Bikin Kar?ar Ahmed Musa A Kano Pillars

Kyaftin ?in Najeriya Ahmed Musa ya cimma yarjejeniyar komawa tsohuwar ?ungiyarsa ta gida, Kano Pillars inda zai taka mata leda har zuwa ?arshen kaka.

Daga cikin sharu?an da aka cimma da shi kafin cimma yarjejeniyar akwai damar iya barin ?ungiyar a duk lokacin da ya samu inda zai koma a Turai.

Ya ce zai bugawa Pillars ?in ne domin ha??aka wasanninsu da martabarsu da kuma taimakawa shi kansa ya ci gaba da zama cikin kuzari, yayinda yake laluben kulob ?in da zai saye shi a Turai.

Ahmed Musa na ?o?arin ganin yada zai ci gaba da zama kan ganiyarsa zuwa wasannin samun gurbi a gasar cin kofin duniya da za a soma a watan Yuni.

?an wasan mai shekara 28, ya bar ?ungiyar Al Nassr ta Saudiyya a watan Oktoba, kuma tun daga wannan lokaci yake samun tayi daga ?asashen Ingila da Rasha da Turkiyya.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da shugaban league na Najeriya Shehu Dikko ne suka bashi shawarar daukan wannan mataki.

Related posts

Leave a Comment