Sauya Akanta Janar: An Rufe Daki Da Barawo

Biyo bayan matakin da Ministan kudi Zainab Ahmed ta ?auka namaye gurbin dakataccen babban akanta Janar Ahmed Idris da Anamekwe Chukwunyere Nwabuoku, sakamakon zargin bada?alar Biliyan 80.

Wani babban abin takaici, shine yadda sabon Akanta Janar din Anamekwe Nwabuoku ke fuskantar wasu tuhume tuhume a gaban hukumar ya?i da rashawa EFCC kan ?atan wasu ma?udan ku?ade lokacin da yake rike da mu?amin Daraktan ku?i na ma’aikatar tsaron Kasa.

Sannan ana zarginsa da aikata al-mundahana a dukkanin ma’aikatum tarayya da yayi aiki a ?angaren kudi, wanda tuni hukumar EFCC ta kwace wasu daga cikin manyan kadarorin sa.

Tambayar da ‘yan Najeriya ke yi a yanzu ita ce me yasa Ministar Ku?i ta dauko irin wannan mutumi da hukumar EFCC take bincike kan aikata ba daidai ba ta bashi wannan matsayi?

Related posts

Leave a Comment