Saudiyya Za Ta Samar Da Daidaito Tsakanin Maza Da Mata A Fannin Aiki

Ma’aikatar Ci gaban al’umma ta Saudiyya na aiki kan wata manufa mai ya?i da nuna wariya da za a fara amfani da ita a kasar nan ba da jimawa ba, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.

A cewar jaridar, manufar, wadda za ta haramta nuna wariya, irinta ce ta farko a kasar. Ta kuma ce ana matakin ?arshe na shirya ta kuma za a amince da ita nan ba da jimawa ba.

Kwanan nan ne hukumomin ?asar suka samar da wani tsari na kai ?arar masu nuna wariya a wuraren aiki.

Haka kuma, ma’aikatar na ?o?ari wurin kawo ?arshen nuna wariyar jinsi a biyan albashi da ?aukar aiki.

Ma’aikatar ta jaddada cewa duka ?an ?asar na da ?ancin yin aiki ba tare da nuna wariyar jinsi ko wani abu na daban ba. Don haka wuraren aiki su rika daidaito a lokacin ?aukaraiki ko wajen tallar guraben aikin.

Gargadin ma’aikatar ya zo ne bayan da wani kamfani ya wallafa gurbin aiki ga maza zalla.

Ta ce wannan ya sa?a wa dokokin ?wadago na ?asar, kuma ta ce ko wane ?an ?asa mace ko namiji na da ikon yin duk aikin da ya so ya yi.

Saudi Crown Prince

Related posts

Leave a Comment