Kano: Hisbah Na Neman Jaruma Umma Shehu Ruwa A Jallo

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Hukumar Hisbah ta jihar ta ce tana gayyatar tauraruwar fina-finan Kannywood, Ummah Shehu, domin ta yi mata karin bayani bisa zargin da ta yi wa wasu jami’anta.

Babban Kwamandan rundunar, Harun Sani Ibn Sina, ya shaida wa BBC Hausa Cewar, suna neman tauraruwar ne bayan da ta yi zargin cewa jami’an Hisbah suna aikata laifuka amma sun ki duba nasu suna takurawa talakawa marasa galihu.

Wasu rahotanni sun ambato tauraruwar tana yin raddi ga hukumar Hisbah bayan da ta kama kama wata ?ar wasan Kannywood da kuma ta yi fice a kafar sada zumunta, Sadiya Haruna, kan “ya?a hotunan batsa” a shafukanta na sada zumunta.

Rahotannin sun nuna cewa Ummah Shehu ta fusata matuka kan matakin da Hisbah ta dauka inda ta yi zargin cewa hukumar ta fi mayar da hankali wajen hukunta talakawa da ‘yan fim bayan kuwa masu hannu da shuni da kuma jami’an hukumar suna tafka ta’asa ba tare da an yi musu hukunci ba.

Sai dai mun yi yunkurin jin karin bayani daga gare ta amma ba ta amsa kiran wayar da muka yi mata ba.

Amma Babban Kwamandan rundunar, Ibn Sina, ya ce suna neman Umma Shehu domin ta yi musu bayani dalla-dalla kan zarge-zargen da ta yi musu.

A cewarsa, idan ba ta je ta yi musu bayani kan batun ba za su kai kararta a gaban kotu inda za su tuhume ta da laifin yi wa Hisbah kazafi.

Ibn Sina ya ce “ba wai muna nemanta ruwa a jallo ba ne; abin da muke cewa shi ne ta zo ta yi mana karin bayani kan zarge-zargen da ta yi mana domin kowa ya sani.

“Idan abubuwan da ta fada na bukatar bincike za mu bincika, idan kuma ta kasa gamsar da mu, to za mu kai ta kotu domin zargin yi mana kazafi.”

Related posts

Leave a Comment