Sarakunan Yarbawa Na Bayan Takarar Tinubu – Sarkin Oyo

Rahotanni daga Ibadan babban birnin Jihar Oyo na bayyana cewar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi a ranar Lahadi, ya ce ya na da tabbacin cewa magabatan Yarabawa za su bai wa jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu nasarar zama shugaban kasar Najeriya a 2023.

An ruwaito Bola Tinubu ya ziyarci basaraken mai daraja ta farko na kasar Yarabawa a fadarsa da ke Oyo a ranar Lahadi domin neman Tubarraki.

Rahotanni sun tabbatar da cewa shugabannin su biyun sun shige ganawar sirri bayan da tsohon gwamnan jihar Legas din ya isa fadar babban basaraken. Jigon jam’iyyar APC din har a halin yanzu bai zanta da manema labarai ba kan abinda ya kai shi masarautar duk da an sakankance cewa ya je neman goyon bayan basaraken ne wurin neman kujerar shugabancin kasa a zabe mai zuwa.

Ahmed Bola Tinubu wanda ya ke daya daga cikin masu bu?atar samun tikitin takarar shugabancin kasa a jam’iyya mai mulki a zabe mai zuwa, ya sanar da burin hakan a wataan Janairu bayan da ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari domin bayyana shirinsa na takarar shugabancin kasan.

Related posts

Leave a Comment