Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya yi gwamna a jihar Kano sau biyu ya yi wa manyan jam’iyyun siyasar Najeriya watau PDP da APC wankin babban bargo bisa gazawarsu a mulki.
Madugun na Kwankwasiyya ya ce jam’iyyun biyu duk ba su da abubuwan da za su nuna domin al’ummar kasar nan su zabe su a 2023.
Kwankwaso ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi hira da gidan rediyon Nasara FM ranar Lahadi 20 ga watan Fubrairu shekarar 2022.
A cewar Rabiu Musa Kwankwaso, jam’iyyarsa ta PDP mai adawa da APC mai mulki, cike suke da ‘yan siyasan da bai dace mutane su sake kada masu kuri’a ba. Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi kira ga al’ummar kasar nan su nemi jam’iyyar da za ta fitar da su daga cikin halin da wadannan jam’iyyu suka jefa kasar a ciki.
“Ban ga abin da jam’iyyar PDP ko APC za su nuna, ko su fadawa ‘Yan Najeriya ba domin su gamsu, su zabe su a zabe mai zuwa na 2023 ba.” “Saboda haka ina tunani mutane su zauna, su yi tunanin jam’iyya da mutanen da ya dace su zaba domin ceto su daga halin da aka shiga.”
