Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na II ya zama jagoran ?ari?ar Tijjaniya a Najeriya, shugaba kuma uba ga duk wani ?an ?ari?ar Tijjaniya a tarayyar Najeriya.
An yi wannan na?i ne a babban taron Maulidin ?asa da ke gudana a jihar Sakkwato cibiyar Daular Uthmaniyya a tarayyar Najeriya.
Babban ?an jagoran Tijjaniya na Afirka Khalifan Ibrahim Inyass ne ya jagoranci bikin na?a tsohon Sarkin na Kano Muhammadu Sanusi wannan babban mu?amin.
Sanusi Lamido Sanusi ya gaji kakansa, Muhammadu Sanusi, wanda shine Khalifan Tijjaniyya na farko a Najeriya, wanda aka na?a shi bayan sauke shi daga karagar mulki da tsohuwar Gwamnatin Arewa ta yi a shekarar 1963.
Bayan rasuwar Tsohon Sarkin ne a shekarar 1990 sai aka na?a Sheikh Isiyaka Rabi’u a matsayin Halifan Tijjaniya a Najeriya, wanda ya jagoranci Shugabancin ta har zuwa lokacin rasuwarsa a shekarar 2018.
Tun rasuwar tsohon Khalifan Tijjaniya, Sheikh Khalifa Isyaku Rabiu a 2018, ba’a nada wanda zai maye gurbinsa ba sai yanzu. Taron ya samu halartar manyan shugabannin ?arikar Tijjaniya a Najeriya da kasashen ketare.
