Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Samuel Aruwan, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida ya hadu da fushin iyayen ?aliban da aka sace a ranar Litinin lokacin da ya ziyarci Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Kwamishinan ya jagoranci wata tawaga zuwa Maramara a cikin Karamar Hukumar don kan sace daliban Makarantar Sakandaren Betel da aka yi, amma sai ya gamu da farmaki daga fusatattun iyayen ?aliban.
An ruwaito cewa wasu ‘yan Bindiga dauke da muggan makamai ne suka kutsa cikin makarantar da safiyar ranar Litinin inda suka sace dalibai 121 yayin da suka kashe sojoji biyu.
Sa’o’i bayan faruwar lamarin, Aruwan ya ziyarci jama’ar yankin amma fusatattun iyaye da masu zanga-zanga suka tare ayarinsa suna masa ihu: “Ka koma! Ka koma! ”.
Jami’an tsaron dake tare da kwamishinan sun yi kokarin kwantar da hankalin masu zanga-zangar amma lamarin ya ci tura. Yayin da ihun ya ci gaba, motocin dake cikin ayarin Aruwan sun juya baya daga wurin hakazalika mutane suka yi ta ihu baki daya.
Wasu mutane sun yiwa kwamishinan izgili kuma sun kafta tafi tare da nuna goyon baya ga iyayen da suka fusata.
